(ABNA24.com) Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Amir Hatami ne ya bayyana cewa; sojoji Iran suna cikin shiri kuma suna sa ido akan duk wani motsi na makiya a cikin wannan yankin da ma duniya baki daya, don haka za su iya dakile duk wata barazana da ke tafe.
Ministan tsaron na Iran ya bayyana haka ne a yau Alhamis a yayin wani zama da ma’aikatar tsaron ta yi domin tattaunawa taken da aka bai wa wannan sabuwar shekarar ta Iraniyawa wato; “Shekarar yin hobbasa a fagen kere-kere”.
Ministan tsaron na Iran ya sanar da cewa; Ruhi na jihadi da juyin juya hali ne ginshikin da za bunkasa kere-kere a kansu, haka nan kuma kyakkyawar sanayya akan barazanar da tsarin musulunci ya ke fuskanta.
/129
25 Afirilu 2020 - 08:04
News ID: 1029565

Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Amir Hatami ne ya bayyana cewa; sojoji Iran suna cikin shiri kuma suna sa ido akan duk wani motsi na makiya a cikin wannan yankin da ma duniya baki daya, don haka za su iya dakile duk wata barazana da ke tafe.